Tuesday, January 20, 2009

YABON GWANI YA ZAMA DOLE

ZUWA GA
PROFESSOR ABDALLA UBA ADAMU

DAGA

RAMADAN UMAR IDRIS




GABATARWA.
NAYI YUNKUNRIN SAMARDA LITTATTAFAN KARANTAWA.
YA YI HUDDUBAR WAYARWA DA SAMARI KAN SU WAJEN KIMIYYA DA FASAHA.
­YADDA YAYI KOKARIN KOYAMIN DAIDAITA KA'IDOJIN RUBUTUN BOKO.
YA GYARA MIN KA'IDOJIN RUBUTU AKARNI NA 20.
TARON KARA WA JUNA SANI NA KUNGIYAR (HAWAN) NA MARUBUTAN HAUSA.
YA SANAR DA KA'IDOJIN RUBUTUN HAUSA.
RUBUTUN WASIKA.
RUBUTUN INSHA'I.
RUFEWA ADDU’A







GABATARWA.
Da sunan Allah mai rahama mai jin kan bawan sa, mai kashewa, mai rayawa, mai kuma azurtawa,mai talautawa, ga wanda yaso, Allah kai mana rahama ka kuma bamu ilimi mai amfani wanda muke kokarin nema a yau da kollon. A yau nake kokarin rubutu nawa mai taken abinda na karu dashi a profeessor Abdalla Uba Adamu, wanda nafi kira (kawuna) .
Babu shakka, asan nu, a hankali idan ana biye dani zan fadi
muhimman abubuwa dana karu dashi, a rayuwata, wanda
kadan zani tsakuro, domin abinda na karu dashi abubuwa ne
muhimmai, wanda da da'akwai lokaci, sai nayi takarda shafi dari biyar.
to amma cikin ikon Allah, zani dan tsakuro kadan daga cikin abinda
na karu dashi a rayuwata insha Allah.
Abinda na karu dashi, a rayuwata Babu shakka kotan tama idan nace na samu wani muhimman ilimi Yawan gaske cikin rayuwata
Da farko kafin na mutsunduma a cikin wannan bayani nawa ina so
Na fadi ma'anar abinda ake kira da orthography. Orthography kamar
yadda sunan yanu na ma'anar wannan kalmar shine rubutu na yau
da kullum. Wannan shine ma'anar orthography a takaice.
Idan na koma kan jawabin nawa ma itaken abinda na karu dashi a
Rayuwata , babu shakka na sami muhimman abubuwan da
Ba don professor abdalla ba to da sam ba zan san’suba, yanzu zamu dauki bayanai babi-babi domin na fadi irin abinda na karu
dashi a cikin hausa kowane babi.

A.NAYI YUNKUNRIN SAMARDA LITTATTAFAN KARANTAWA.

Idan muka dubi wannan sashi, babu shakka na karu da muhimmam
Ilimmai, masu yawa, domin ta cikin wannan sashine, na san wacce
irin wuya ko kuma wahalhalu aka sha wurin yunkurin samar da
littattafan karantawa. Inda muka san Professor Abdalla, wato kawu na, kuma Muka san irin yun kurin da yayi domin asa marmana da ilimi ga ya’yan hausawa, da kuma kishin su da yake yi, a fadin duniya, Domin mu wannan lokacin duk rubuce-rubucen da muke dasu to da Yanar gizo-gizo, da ake rubuta su wannan babi shine yake sawa a rubuta, kuma ya rubuta da kansa, domin yasa nar damu abin yake faruwa fadin duniya don mu samu damar karantawa. Misali idan muka dobi hausa character, zamu ga shine babban mai da tallafi wajen yin wannan character koma muci shi yayi, wacce ba’a najeriya kadai ake amma da ita ba. A shekara ta dubu biyu da kwas (2008) a cikin watan sha biyu ne, yaji wata kasa mai suna Jamus,wacce a turanci ake cimata Germany,wanda shararrin marubucin Ado mahd gidan dabino, ya rakashi har kasar jamus. makasuddin zuwan shine, ya jine domin yayi bayani akan adabin hausawa,wanda turawan da yaje yiwa bayanin, kuma sun gamsu sosai da sosai .wanda muke kara godewa Allah da ya dawu mana dashi lafiya, doda na san mutan ne mai yawan ciwan amma acan ko ciwan kan bai yiba, na kara dogewa Allah sosai-sosai da ya dawu mana dashi lafiya.

YA YI HUDDUBAR WAYARWA DA SAMARI KAN SU WAJEN KIMIYYA DA FASAHA.

Babu shakka a wannan babi samari daya wa na sami ilimi domin na san yadda aka sami matsaloli saka makon kan garewar kimiyya a kasar hausa ko kuma nace karanchin kimiyya .
Idan muka duba irin huddobar da, Professor Abdalla, da yayi, a wata jamiyya a mai aminu kano college of education wacce aka fi da suna (legal) wacce a cikin shekara ta dubu biyu da shida, (2006) wacce yayi maganar akan matsayin musulumi a kimiyya da fasaha, wanda a wannan lokaci ne, dalibai suka san mene ne ma’anar kimiyya da fasaha, suka kuma san matsayin musulunci, wannan huddobar ta karawa dalibai da yawa karfin gwiwa, wajen mai da hankalin su, ga kimiyya da fasaha, cimma rayuwar bahaushe gaba a fadin duniya . Ga wasu daga cikin bayanin da yayi a wannan huddobar tasa da yayi a wannan jamiyyi’a.wajen yin amfani da wasu kalmomi na turanci suka kuma na hausa domin ya sanarwa da dalibai matsayin kimiyya da fasaha a hausance.

YAYI AMFANI DA KALMOMI KAMAR WANNAN

· komai nesan jifa kasa zai fado ((Law of gravitation in Physics)
· Idan guga ya dade a rijiya, to zai zo da ruwa da yawa (Capillary rise of liquids in Biology)
· Ruwa ba ya tsami banza (Impurities in Chemistry)
· Alheri danko ne, ba ya faduwa kasa banza (cohesion in Physics)
· Lissafi ko ya kwana a dawa, kura ba ta cinsa (Conservation)
· Hali zanen dutse (genetics)
· Ilimi garkuwar dan Adam (application of knowledge)
· Lafiya uwar jiki (health)
· Rigakafi ya fi magani (health)
· Karfe daya ba ya amo (metallurgy)
· Da zafi zafi a kan bugi karfe (metallurgy)
· Kanwa uwar gami (catalyst)
· Idan ba kira, mai ya ci gawayi (equilibrium)


Toko a nan muka tsaya babu shakka mun amfanu da
nagartaccen ilimi amma ada can bamu san matsayin wadannan kalomomi ba a hausance wannan garabasar tawu ce nesa ba kusa ba don haka nema na ke godewa Allah subuhanahu wata’ala da yake ta ja mana ransa har yanzu bai karba ba.

D.YADDA YAYI KOKARIN KOYAMIN DAIDAITA KA'IDOJIN RUBUTUN BOKO.

Duk wannan ilimi da na samu, bai barni haka ba, Sai da ya ga ya nuna min, yadda aka daidaita, duk dukkan nin ka'dojin rubutun boko inda yanda na sani adacan bamu da, B, D, K, TS, Y da kuma yadda ake raba wasu kalmomin, da yadda ake hadasu misali, idan
zamu rubuta saboda, sai mu rubuta sa boda, da sauransu amma cikin hadu wata da kawuna,wannan abin ya zamar min ruwan dare, domin na same wannan ilimi mai tarin yawa, da kuma amfani ai duk mutumin dabai san matsayin Professor Abdalla a kasar hausa ba, koda baya yin book, to ya chi ayi masa jaje, saboda ko mutun baya karantar book, ya kamata a ce kasan wannan bawan Allah, saboda mutun ne mai yawan amfani a cikin al’umma.

YA GYARA MIN KA'IDOJIN RUBUTU AKARNI NA 20.

A wannan sashine ilimin dana karu dashi yawu ce misali, domin
na san irin gwagwarmayar da aka sha, wurin samuwar, B, D, K, domin sutsaya da kafarsu. Inda har na iliman tu da sunan wasu mashahuran turawa wato C C H ROBINSONG da kuma FRANK EDGAR da kuma irin Gudun mawar daya bani wurin samuwar B, D, K na kuma karu dashi ba sai da aka yi musu wani gyaraba na kuma karo da wasu . sababbin bakake daza'a dinga amfani dasu, CH, CH a dinga yin su kamar haka. CH ta koma matsayin C, CH kuma C wannan kurin ilimine domin idan ban san suba sai dai nai tayi ta baragada ta wajen rubutun hausa.


TARON KARA WA JUNA SANI NA KUNGIYAR (HAWAN) NA MARUBUTAN HAUSA

Idan na dubi yadda aka kafa hukumar hausa ta (hawan) to a nan ma ilimin da na karu dashi yana da yawan gaske.
Yanzu babu abinda zan cewa professor Abdalla Uba Adamu uban kungiyar (hawan) wato (kawuna) sai dai nace masa Allah ya saka masa da alkairi, domin sanina da profeesor Abdalla Uba Adamu shi yasa ma har na wane ne (BAUSHE), kuma wacce irin gudun mawar daya bayar musamman ta wurin bada shawarar a kafa hukumar hausa wacce ita zata tantance tsantsar Al’adun ganganriyar na (BAUSHE) . Bayan haka na da sanin wasu mashahuran mutane da suka bada gudun mawar su wurin ganin wannan hukuma tachi gaba ba zani man ce da irin wannan mutane ba irin su.

1. Professor Isa Muktar
2. Ado Ahmad Gidan Dabino
3. Amina


Kuma na iliman tu da ayyu kansu da yawan gaske daga ciki .
akwai :-
1. Takardarta ka'idojin rubutun hausa RULES FOR HAUSA
SPELLING wanda sharararreyar marubuciyar ta rubuta shi mai suna (Amina) A cikin wannan taro na karawa juna sani.

2. Daga cikin bayanin Professor Isa Muktar yayi, na karu da shi wajen cimma yar jejeniyar, wasu kalmomi, da ya bayyana na hawun hausa,

misali
ismi ya koma suna, sai kuma fi'ili amsi ya koma matsayin abinda za'ayi, wato future tense, a turanci .
3. Ya kuma yi bayani da ake amfani da wasu kalmomi da duk na aro ne a rubutun hausawa na zamani .
wanda ake kiransu da turanci suna kamar haka, ALPHABETICAL LIST OF WORDS IMPORTED INTO HAUSA . Bayan nan dama anyi ayyuka masu amfanin gasket, to ai ko a nan tsaya, sai hamdala domin (kawuna) ya fitar dani kunyar rashin sanin halinda rubutu da marubuta suke ciki.

Idan aka tambayi ni menene ka'idojin rubutun hausa,
a shekarun baya, ya zama dole nayi jugum, badon komai ba,
sai domin ban san shiba, amma cikin ikon Allah saka makon
haduwa ta da Professor Abdalla, sai gashi na san ka'idojin rubutun hausa, da kuma dalilin da yasa aka yi wannan taron karawa juna sani, wannan dalili kuwa shine, yadda mutane suke rubuta kalmomin hausa barkatai, wasu a rabe wasu hade, ga sunan dai bai kamata ba, domin babu tsari wannan daliln shine yasa.
har'akayi taron daidaita ka'idojin rubutun hausa.
In dahar na duba labarin Professor Abadalla ya bani na karanta anyi taro harguda uku.
Na farko a birnin (Bamako) dake kasar mali ranar 28 na watan fabrairu zuwa 5 gawatan maris nashekara 1966.
Taro na biyu anyi shine a jamiar (Ahamadu Bello) dake zariya (A.B.U) ranar 21 gawatan yuni nashekara 1970.
Sai taro na uku da'akayi a jamiar (Bayaro) dake kano (B.U.K) a watam satumba a shekara (1972) .

To yanzu wannan abin a rzikin na hausa daya faro bamu gamu ba dan dalilin Professor Abdalla ba, ai ba zan san shi ba. Idan an tambaye ni yadda aka yi taron daidaita ka'idojin rubutun hausa.
A cikin dai wannan babin na iliman tu dawa su muhinmam darusa masu amfani wanda aka zartar a lokacin wannan taro daga cikin irin wannan abubuwa na samu ilimi wa `yanda gyare gyarene.

kamar haka :----
SABUWAR KA'IDA MAI MAKON

zaka za ka

koyaushe ko yaushe

kowane ko wane

ko'ina ko ina

itace i tace
menene me nene

Da sauran gyare gyare mahimmai wa `yan da daba ban san Professor Abdalla ba, ai da nayi babbar asarar muhimmin ilimi mai'anfani.
Acikin dai wannan babin na ilimantu, da sanin wata irin matsala
Da mutanan nijar suka kawu ta, inda dole yasa aka yi muihimmin taro abirnin (Yamai), a cibiyar waririn ta harshe da tarihi ta sarrafa adabin baka wato (CENTRE FOR LINGUISTIC AND HISTORICAL STUDIES BY ORAL TRADITION), karkashin jagorancin majalisar
Hada kan Africa wato (O. A. U), daga ranar 7 zuwa 12 na watan janairu 1980.
To ai wannan irin ilimin sai dai na godewa Allah, domin wannan irin dimbin ilimin dana samu a kan hausa orthography.
A cikin irin abubuwan dana amfana wanda a kafi to dashi sun
Hadar da tsara duk ka'idojin rubutun hausa, wanda aka
Tacesu.
kamar haka :----

MANYAN BAKAKE.

B, B, C, D, D, F, G, H, J, K, K, L, M, N, R, S, T, W, Y, Y, Z

KANANAN BAKAKE.

b, b, c, d, d, f, g, h, j, k, k, l, m, n, r, s, t, w, y, y, z.

WASULA.
KANANA
a, e, i, o, u.


MANYA
A, E, I, O, U,


AURAN WASULA

KANANA

ai, au.
MANYA
AI, AU.


TAGWAYAN WASULLA

KANANA
fy,
MANYA
FY, GW, GY, KW, KY, KW, KY, SH, TS.

Wayan wa dan dama wasu sauran ka'idoji masu tarin yawa toko wannan babinan na amfana dashi ai naci ribar Professor Abdalla
Ilimin da na samu sai dai ham’dala da godiya ga Allah.

YA SANAR DA KA'IDOJIN RUBUTUN HAUSA.

Na iliman tu wasu ka'idojin rubutun hausa, wanda koda yake na sansu tun'a Primary to amma Professor Abdalla ya kara min
Bayanai, masu tarin yawan gaske wadan nan ka'idojin sune.

Kamar haka:-

1. Wakafi (,)

2. Wakafi mai ruwa (;)

3. Aya (.)

4. Tagwayan ayoyi (:)

5. Ayar tambaya (?)

6. Ayar motsin rai (!)

RUBUTUN WASIKA.

Kamar yadda turanchi yake da irin nasa ka'idojin rubutun wasika
wato (LETTER WRITTEN) to nima Professor Abdalla bai barni
a haka ba sai daya fito min da irin namu rubutun wasikun da kuma
sunayen su daya bayan daya ga
misali.
1. Wasikar aboki

2. Wasikar neman aiki

Da sauransu.

Na kuma kara samun ilimi da daman gaske a kan wannan babin
ko yanzu bana shayin ayi min tambaya a kan rubutun wasika.

7. Ayar bude magana ('')

8. Ayar rufe magana (")

9. Baka biyu {()}

10. Karan dori (--)

11. Zarce (------)


Yanzu idan ban da Professor Abdalla yaya zani san wani abu
Wai shi karan dori ko zarce ko baka biyu da sauransu.
To ai Professor Abdallah babu abinda zace da kai Sai dai Allah ya kara mana sanin juna .


RUBUTUN INSHA'I.

Shi kuma wannan babin sai dai sam barka, domin daya da ban
san menene insha'I, ba ballan tana yadda ake rubutun sa, babu
shakka ya zamen men jagora, akan dukkannin wasu matslolin hausa da yadda zani warware su domin.
Haka ya zame mana garkuwa dubi dai yadda wannan babin
yasa nar dani rubutun insha'i da kuma shi kansa insha'in da yadda
ake rubuta shi, da yadda dokokinsa, da ka'idojinsa suke, ai ni dai san barka, sai nace Allah ya kara dan kun zumunci, Allah ya barmu tare amin summa amin.
POSTE BY RAMADAN UMAR IDRIS



1 comment: